Yan bindigan da suka raunata tare da kwace mota da wayoyin Hon. Bala Kalu sun Shiga hannu

Yan bindigan da suka raunata tare da kwace mota da wayoyin Hon. Bala Kalu sun Shiga hannu


Daga: Muhammad Suleiman Yobe

An Kama ƴan bindigan da suka raunata tare da kwace mota da wayoyin Hon. Bala Kalu.

Hukumar ƴan Sanda a jihar Adamawa tayi nasaran damƙe ƴan bindigan ne biyo bayan wani bincike da sukayi a faɗin jihar.

Idan ba'a Manta ba, a daren ranar Litinin 11 ga Febrairu ne wasu ɓata gari suka far ma ɗaya daga cikin kwamishinonin gwamnatin jihar Adamawa, na ɓangaren Muhalli wato Hon. Bala Kalu a Jimeta, inda sukayi masa raunuka, suka kwace motarsa da woyoyin hannunsa.




Post a Comment

0 Comments