Yankin Yarabawa Kudu Maso Yamma sun nemi a kirkiro wasu karin Jihohi
An gabatar da kudirin dokar da ke neman a kirkiro karin wasu jihohi uku a yankin Kudu maso Yamma a zauren majalisar wakilai ta Najeriya,
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Obokun/Oriade na jihar Osun, Oluwole Oke ne ya gabatar da kudurin dokar mai neman a ƙirƙiro jihohin Oke-Ogun da Ijebu da kuma Ife-Ijesa.
Dokar da aka gabatar anyi mata take da “Kudirin doka don gyara kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya 1999 (kamar yadda aka gyara)”,
Mahanga ta ruwaito a cikin daftarin kudirin dokar, jihar an gabatar da cewa sabuwar jihar Oke-Ogun ita ce jiha sai Iseyin a matsayin babban birnin jihar, sannan za ta kunshi kananan hukumomi 12 da suka hada da Olorunsogo, Irepo, Oorerelope, Ogbomosho North, Ogbomosho South, Saki-East, Saki-West, Atisbo, Itesiwaju, Iwajowa, Kajola da kuma Iseyin.
Sai sabuwar jihar Ijebu idan aka kirkiro ta za ta kunshi kananan hukumomin Ijebu ta gabas, Ijebu arewa maso gabas, Ijebu Ode, Ikenne, Odogbolu, Ogun Waterside, Remo North da Sagamu sannan Ijebu Ode ce zata zama babban birnin jihar ta Ijebu.
Har ila yau Mahanga ta ruwaito a cewar Oke, wanda ke shugabantar kwamitin majalisar kan harkokin shari’a, jihar Ife Ijesa za ta kasance da kananan hukumomi 11 da suka hada da Atakunmosa ta gabas, Atakunmosa ta yamma, Boluwaduro, Ife ta tsakiya, Ife East, Ife North, Ife South, Ilesa Gabas, Ilesa ta yamma. , Oboku da kuma Oriade.
Shiyyar Kudu-maso-Yamma dai a halin yanzu ta kunshi jihohi shida, wadanda suka hada da jihohin Ondo, Oyo, Legas, Ogun, Osun da kuma Ekiti.
0 Comments