YANZU-YANZU: Jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky ya Sauka Najeriya

 YANZU-YANZU: Jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky ya Sauka Najeriya

Sheikh Zakzaky a lokacin da suka iso filin da almajiransa suka shirya mashi kyakkyawar tarba

Daga Yahaya Muhammad Soje

Jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Zakzaky wanda ya dauki tsawon sama da wata hubu bayan ƙasar yana ƙasar Iran domin Jinyar harbin da Sojojin Najeriya karkashin jagorancin Buhari suka masa tare da mai dakin sa ya dawo Najeriya bayan samun sauki tare da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim.

Gwamnatin tsohon shugaban kasar Najeriya, Buhari ta Afka ma Sheikh Zakzaky da Almajiransa a watan Disambar 2015, inda aka kashe sama da mutum dubu tare da ƴaƴan Malamin guda 3. Aka kuma kama shi aka tsare shi kafin daga baya aka sake shi amma ba'a bashi fasfo dinsa ba domin fita neman lafiya sai da Gwamnatin ta ƙare.

Cikin hotuna saku iya ganin yanda Almajiransa suka shirya masa Gagarumar tarba a babban filin taron dake 'Stadium' a ƙwaryar birnin tarayya, Abuja.

 







Post a Comment

0 Comments