Yohanna Y D Buru Pastor mai kiran hadin kan Yan arewa musamman Musulmi da Kirista ya halarci bikin tarbar sheikh Zakzaky

 Yohanna Y D Buru Pastor mai kiran hadin kan Yan arewa musamman Musulmi da Kirista ya halarci bikin tarbar sheikh Zakzaky

Pastor Yohanna Y D Buru tare da  Pastor George T John a filin Wasa na kasa da kasa dake Abuja a wajen tarbar Sheikh Photo credit/Pastor YD Buru Facebook


Daga Mahadi Umar kaita

Shahararren pastor din nan Mai Kira da Muryar adalci tsakanin musulmi da kirista Kuma shahararren wajen son hadin kan musulmi da kirista a Arewacin Najeriya Pastor Yohanna Y D Buru Ya halarci bikin tarbar sheikh Zakzaky daga dawowa daga jinya.


Pastor din dai ba wannan bane ba karonshi na farko na hakartar tarurrukan musulmi musamman ma na Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky din tun kafin abunda ya faru a zaria 2015 ya faru.


Pastor Yohanna YD Buru yanada matukan kyakkyawar alaka da musulmi sosan gaske domin ya kasance Mai yawan kira Akan hadin kai Yan arewa dakuma kira da a tashi domin a nemo yanci, wannan ce tasa ya sallamawa Kiran Sheikh Zakzaky domin yaga babban Kiran sheikh din shine Kira domin hadin kan al'umma dakuma yaki da Zalunci.


Pastor Yohanna Y D Buru Zero-Fear And Zero-Hatred bashida wata magana a kafafen sada zumunta data wuce hadin kan musulmi da kirista domin a cikin maganganunsa Yana cewa 👇

A lokachin da aka fiye zubda jini da makiyaya da fulani sukeyi a jihar Kaduna ya fito a kafar sada zumunta inda yake cewa "Don Allah irin zubda jinin A Al'umma jihar Kaduna a shiya ta daya da ta biyu da shiya ta uku bai isa haka nan ba ga wannan gwabnatin, don Allah kawo karshen zubda jinin haka mana?

 Haba jama'a! da kyar a wayi gari ba a zubda jinin dan jihar Kaduna ba, ko a shiya ta uku ko shiya ta biyu ko ashiya ta daya, to, don Allah a dai tuna fa akwai ranar hissabi fa?

A lokacin da akai rikicin kisan Dibera wacce tayi 6atanci ga Manzon Allah (SAW) a Jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya Pastor din ya fito a kafar sadarwa Inda yayi Kira da babbar murya tare da kokarin naiman ayi adalci hakika yayi maganganu masu matukar mahinmanci Wanda suka ja hankalin Al'ummar musulmi da kirista wajen zaunawa lafiya dakuma kwantar da tarzomar da ta kunno Kai .

 Ga rubutun nan 👇

Al'ummah Musulman Nijeriya da na duniya gaba daya ina maku fatan Alkhairi, kuna nan lafiya? 

Masu iya magana sun ce: "tuna baya shine roko."

A shekarun baya watau tsakani 2013 ko 2014 anyi wata fim(film) na batanci ga Manzo Allah Muhammad (PBUH) da mu Kiristan duniya bamu ji dadi ba. Ni na san zafin batanci ga kowane irin addini, domin da haka sai da na jahoranci zanga-zangan na lumana tare Fastoci (Pastors) da Mallamai (Imams) a tsakiyar Musulmai a Tudun Wada Kaduna South dai dai kofar gidan Sheikh Salisu Abdullahi Mai Barota kuma shi Shaida ne, domin nuna bacin ranmu domin ba mu goyi bayan wannan batancin ba.

 A 2015 mujallar Charlie Hebdo na kasar Farasa (France) ta yi rubutun batancin ga Manzon Allah Muhammad (PBUH) ni ne kuma na jahoranci wannan zanga-zangan ta lumana na yin Allah wadai domin rashin jindadi mu kuma duniya sun sani.

 Domin da haka mu ajiye zuciya nesa mu bi ka'idodin sharia domin a sami adalci a shari'ance a ko ina a Nijeriya kuma tsakanin mabambantan addinai. Da Musulmai da Kiristan Arewa muna fuskatan maganan ta'adanci a Arewa da Nijeriya gaba daya domin 2009 ayi wa Imam Muhammad Yusuf shugaban Boko Haram irin kisa killa irinta rashin adalci kuma ta haifar mana da Boko Haram.

Amma da anji shawara da jama'a aka gurfanar da shi a gaban kuliya aka same shi da lafiya, toh, da yau wanke hula bata kaimu dare ba aka magana Boko Haram.

Domin inda anyi wa Imam Muhammad Yusuf shugaban Boko Haram adalci tawurin sharia ne toh, da watakila yau babu wata kungiyar kama Boko Haram a Nijeriya. Amma rashin bin ka'idodin sharia ke harfar da rashin adalci a doron kasa.

Haka ma fitintinu da ke tsakanin Fulani da Manoma a kasar Hausa da ta bazu zuwa sassan Nijeriya duk domin rashin bin hanyoyin shari'ar ta bangare addini ko ta dokokin kasa itace ta haifar da fitintinu a Arewa.

Da da manoma ko Hausa da makwabtansu Fulani ko makiyaya anyi masu adalci ne tun farko tawurin yin shari'ar gaskiya tsakanin su ko a sasantasu ko tawurin sasantawa na gaskiya toh, da babu Barayin daji ko masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a Arewa.

Domin da haka ina kira ga ilahirin Musulmai da Kiristan Arewa da mu dawo cikin hayacinmu, mu koma ga Allah da kuma koysuwan addinanmu da kuma tafarkin shari'un addinanmu mu, mu kuma yiwa junanmu adalci domin fahimtan juna, kyakyawan zamantakewa domin samun dawamamen zaman lafiya.

Abinda ya faru akan kisan Deborah Emmanuel ko Deborah Samuel ba a bi ka'idodin shari'ar Musulunci ba ko na dokoki kasa ba, amma kam bamu goyi bayan sabo ko batanci ga kowane irin nau'in addini a doron kasa. In an bi ka'idodin sharia toh, babu masu cece-kuce akan hukuncin da sharia ta tabbatar da ita. 

Adalci tana samuwa ne in an bi ka'idodin sharia ko dokar kasa.Yah Allah Ubangiji ka yafe mana laifufukanmu."

Hakika wannan rubutun da Pastor Yohanna Y D Buru yayi matukar Bada gudummuwa wajen zaman lafiya musamman a yacce kafin yayi wannan Kiran an tunzura mutane har ana tunanin rikicin addini zai iya 6arkewa a jihar ta Sokoton Wanda hakan na iya jawo asarar rayuka masu tarin yawa.

Haka zaluka pastor din Yana ziyartar tarukan addini na kowace mazhaba ta Addinin Musulunci idan aka gayyaceshi batare da wariyar akida ba ko bangarenci.

Pastor Yohanna Y D Buru a sahun Mauludin Annabi da aka gudanar  Nasarawa Kaduna south

Post a Comment

0 Comments