Za mu haɗu da Sadiya Marshall a gaban shari'a idan ba ta janye kalaman ɓatanci a kan Hon. Yusuf Gagdi da matarsa Layla Ali Othman ba nan da kwanaki uku - Lauyoyi
Jaridar Muryar Labarai ta samu kwafin wata takarda mai shafi (5) wacce aka buga a ranar 31 ga watan Janairu ɗauke da sa hannun N.U Usman Esq, da ke buƙatar Sadiya Ahmed Marshall ta fito fili ta janye kalaman ɓata suna da ta yi a (Social Media) a kan Onarabul Yusuf Adamu Gagdi da matarsa, Hajiya Laylah Ali Othman sannan kuma ta nemi gafararsu nan da kwanaki uku kacal in kuma ta ƙi to za su tsaya da ita a gaban shari'a su nemo wa waɗanda suke karewar haƙƙoƙinsu.
A cikin takardar masu shigar da ƙaran sun yi nuni da cewa ba su gamsu da haƙurin farko da Sadiya Marshal ta bayar ba. Ya zama wajibi a gare ta yanzu ta fito ta ƙaryata kanta ta kuma nemi gafara.
Sun ƙara da cewa Onarabul Adamu Gagdi ɗan siyasa ne kana kuma shugaban al'umma mai daraja wanda yake wakiltar garuruwan Pankshim/Kanam/Kanke na Jihar Filato a majalissar tarayya.
Yayin da a gefe guda kuma, Hajiya Laylah Ali Othman ke zaman babbar mace mai daraja kana hamshaƙiyar ƴar kasuwa da ke zaman mamallakiyar katafaren gidan abinci na (L&N Kitchen) da katafariyar masana'antar ƙera kayayyakin ɗaki ta (L&N Interios/Furniture) da sauran nau'ikan kasuwanci daban-daban a ciki da wajen Abuja. Sannan kuma tana da ɗumbin abokan hulɗar kasuwanci (kwastomomi) ɗaiɗaikun mutane har ma da kamfanoni da sauran hukumomi da ma'aikatu.
Amma duk da haka Sadiya Marshall ta fito fili ta hau kan manhajar (Facebook) tayi Bidiyo a ranar 27 ga watan 1 na shekarar 2024 ta keta alfarmarsu ta yi maganganun cin zarafi da ɓata musu suna a gaban mabiyansu da kwastomominsu da ma sauran al'umma gabaɗaya wanda hakan zubar musu da mutunci ne tayadda za ta haifar musu da matsala a harkokinsu na siyasa da harkokinsu na kasuwanci.
Jerin laifuffukan da masu shigar da ƙaran suke tuhumar Sadiya Marshall a kai tare da neman ta fito ta janye kalamanta ta kuma nemi gafara ko su haɗu da ita a gaban ƙuliya manta sabo sun haɗa da:
1. Neman Gurgunta Kasuwancin Wacce suke kare wa (Hajiya Laila Ali Uthman): masu shigar da ƙarar sun ƙara da cewa suna tuhumar Sadiya Marshall da neman gurgunta kasuwancin Hajiya Laila ta hanyar kore al'umma daga sayen kayayyakinta wanda a cikin bidiyon ɓata mata suna da ta fitar ta zargi Lailan da rashin gaskiya. Da zarginta da zuba kayan maye a cikin abincinta domin ta ja hankalin abokan cinikayyarta.
2. Zargin Tunzura Mata Su Bijirewa Maza: zargi na biyu da masu shigar da ƙarar suke tuhumar Sadiya Marshall a kai shi ne ta zargi wacce suke kare wa (Hajiya Laylah Ali Othman ) da yaɗa da'awar tunzura mata su bijirewa maza (Feminism) wanda hakan saɓa wa da'awar Manzon Allah (S.A.W) ne.
3. Zargin Zina Da Neman Kashe Aure: masu shigar da ƙarar sun ƙara da cewa Sadiya Marshall ta zargi wacce suke kare wa (Hajiya Laylah Ali Othman ) da laifin zina tare da neman kashe mata aure dangane da zargin da tayi cewa wai Hajiya Laylah ta je gidan gyaran hali na Kuje da kayan laifi ta haɗu da ɗaurarre, Abdurrashid Maina. Tare da zarginta da kwanciya da mazajen da ba nata ba tana samun kuɗaɗe da kyaututtuka wanda hatta gidanta ta wannan hanyar ta same shi.
4. Zargin Auren Jari: masu shigar da ƙara sun ƙara da tuhumar Sadiya Marshall da zargin cewa ta zargi wacce suke karewa (Hajiya Laylah Ali Othman ) da auren mijinta Onarabul Yusuf Gagdi saboda kuɗinsa, shuhurarsa a siyasa da ƙyale-ƙyale gami da neman ɗaukaka.
5. Zargin Kafa Gidauniyar Bogi: suna kuma tuhumar Sadiya Marshall da zargin wacce suke karewa (Hajiya Laylah Ali Othman ) da kafa gidauniyar taimakon al'umma ta bogi saboda ta cimma buri a daidai lokacin da take son auren mijin nata, Onarabul Yusuf Gagdi tare da rage shekarunta na haihuwa daga 46 zuwa 34.
6. Zargin Yaɗa Hotunan Tsiraici: Suna kuma tuhumar Sadiya Marshall da zargin wacce suke karewa (Hajiya Laila Ali Uthman) da yaɗa hotunan tsiraici.
A ƙarshen takardar, masu shigar da ƙarar sun fayyace cewa duk waɗannan kalamai na zarge-zarge da ɓatanci da Sadiya Marshall tayi a kan waɗanda suke karewa (Hajiya Laylah Ali Othman da maigidanta, Onarabul Yusuf Gagdi) kalamai ne waɗanda suka haifar musu da matsala a siyasa da kasuwancinsu gami da jefa musu damuwa da tashin hankali a cikin zukatansu kuma abokan adawa ne suka ɗauki nauyinta gami manufarta ta ƙashin kanta.
Da wannan dalili ne masu shigar da ƙarar suka nemi lallai Sadiya Marshall ta gaggauta yin amfani da dukkan wasu shafuka na kafafen sadarwa na zamani da manyan jaridun ƙasa ta janye kalamanta ta ƙaryata kanta, sannan kuma ta ƙara da ba da haƙuri da neman gafarar waɗanda suke karewar nan da kwanaki uku. In ko ta kuskura ta haura kwanakin ba ta aikata hakan ba to lallai ba su da sauran zaɓi da ya wuce su nemo wa waɗanda suke karewar haƙƙoƙinu a gaban shari'a.
Hafsat Abdullahi Muryar Labarai
0 Comments