Za'a haramtawa yara shiga shafukan sada zumunta domin kare lafiyar kwakwalwarsu

 Za'a haramtawa yara shiga shafukan sada zumunta domin kare lafiyar kwakwalwarsu



Majalisu biyu na jihar Florida ta Amurka sun zartas da wani kuɗirin doka da zai haramta wa duk wanda bai kai shekara 16 amfani da shafukan sada zumunta.

Masu goyon bayan ƙudurin sun ce hakan zai kare lafiyar kwakwalwar yara, amma gwamnan jihar, Ron de Santis, ya ce yana yin taka-tsantsan kan duk wata doka da za ta ci karo da wadda iyaye suke da ikon kafa wa yaransu.

Akwai fargabar cewa ƙudurin ya saba dokar Amurka ta kundin tsarin mulki da aka yi wa kwaskwarima ta ƴancin fadin albarkacin baki, da kuma dokar da ta ce iyaye ne ke da ikon zartar da hukuncin amfani da shafukan sada zumunta ga yaransu ba gwamnati ba.



Post a Comment

0 Comments