Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya alƙawarta tallafa wa tsare-tsaren manunfofin taimaka wa al'umma da ci gabansu, don magance matsalolin tattalin arziki a jihar Kano.
Dangote ya yi wanna alƙawarin ne a lokacin da ziyarci gwamnan jihar Kano Abba Yusuf a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce Dangote ya ce yana sane da halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke fuskanta.
Dangote ya alƙwarta bayar da tallafi don inganta fannonin lafiya da ilimi da hanyoyin yaƙi da talauci ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.
Attajirin ɗan kasuwar ya alƙawarta yin aiki kafaɗa dakafaɗa da gwamnatin jihar don bunƙasa ci gaban al'ummar jihar.
A nasa ɓangare gwamnan jihar ya gode wa hamshaƙin ɗan kasuwar bisa manyan ayyukan ci gaba da ya samar musamman sashen kula da masu buƙatar gaggawa da ɗakunan tiyata da na haihuwa da na yara a asibitin Murtala da ke jijar.
Sannan kuma gwamnan ya buƙacin Dangote ya tallafa wa jihar don gina tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin farfaɗo da masana'antun jihar don bunƙasa har tattalin arziki da kuma ƙarfafa jihar.
📸Photo:-Kano State Govt
Haka kuma Gwamna Abba Kabir ya shaida wa Dangoten cewa jihar na cikin tsananin buƙatar asibitin kula da masu lalalar cutar sikila domin samar da magunguna kyauta ga masu lalurar.
A ɓangaren ababen more rayuwa, gwamnan jihar ya buƙaci tallafin Dangote don gina tituna na zamani, da gidaje, da ci gaban al'umma da sauran fannoni.
0 Comments