Almajiran Sheikh Zakzaky Sun Ƙona Tutar Amurka a Ofishin Jakadancin Amurka dake Abuja

Almajiran Sheikh Zakzaky Sun Ƙona Tutar Amurka a Ofishin Jakadancin Amurka dake Abuja


Wasu matasa a yayin gudanar da jerin gwanon nuna damuwa da kashe-kashen da ake yi a ƙasar Falasdinu a nan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, sun ƙone Tutar Kasar Amurka a babban ofishin Jakadancin ƙasar dake babban birnin tarayya, Abuja.

Matasan Almajiran Shaikh Zakzaky wanda aka fi sani da yan Shi'a sun yi jerin gwanon nasu a ranar yau Litinin.




Daya daga cikin jagororin zanga-zangar, Abdullahi Musa ya bayyanawa manema labarai cewa, sun fito kenan domin nuna damuwa da halin da al'ummar Kasar Falasdinu suke ciki kuma suna zargin Kasar Amurka dumu-dumu kan abubuwan da ke faruwa.

Inda a karshe ya ce sun far fitowa kenan, zasu ci gaba a kosa yaushe matukar ba'a samu sassauci ba akan abunda ke faruwa da Kasar Falasdinu.

Kalli video anan👇


Post a Comment

0 Comments