An yanke wa ɗan China da ya kashe Ummita hukuncin kisa ta hanyar rataya

 An yanke wa ɗan China da ya kashe Ummita hukuncin kisa ta hanyar rataya



Wata Babbar Kotun Jihar Kano ce ta yanke hukuncin bayan ta samu Geng Quangron da laifin kisan Ummita, a cewar Kwamishinan Shari'a na jihar, Haruna Isa Dederi.

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa Geng Quangron hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe kashe Ummita a Kano.

Antoni Janar na Jihar Kano Haruna Dederi ya tabbatar ƴan jarida da hukuncin kotun a ranar Talata.

A 2022 ne lamarin ya faru wanda ya yi matuƙar tayar da hankalin jama’a.

A lokacin da lamarin ya faru, an zargi ɗan kasar Chinan da bin Ummulkusum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita har gidansu da ke unguwar Janbulo inda ya soka mata wuka wanda hakan ya yi ajalinta.

Daga baya an gurfanar da Mista Geng a gaban kotu inda ya amsa laifin kisan Ummita tare da cewa ya kashe mata kudi sama da naira miliyan 60.

Post a Comment

0 Comments