Dakarun Falasdinu sun aika da saƙo zuwa ga Jagoran Jamhuriyar Musulunci dake Iran

Dakarun Falasdinu sun aika da saƙo zuwa ga Jagoran Jamhuriyar Musulunci dake Iran 


Dakarun Musulunci tsagin Falasdinu sun aike da saƙo zuwa ga Jagoran Jamhuriyar Musulunci dake Iran wato Syed Ali Khamane'i cewa, kada su sa damuwa a ransu, suna dauke da nasarar yaƙin da ake gwabzawa a zirin Gaza da kaso casa'in.

Sunce a rabu da farfagandar duniya da ake yadawa a kafafen sada zumunta, abinda suka fi bukata a yanzu bai wuce Addu'a ba, saboda yaƙinin su da Allah ta'ala cewa yana ji, kuma yana gani, kuma tabbas su zasuyi nasarar yaƙin kamar yadda akaiwa muminai busharar Alƙawari a Alkur'ani mai girma.

Ya Hayyu ya Qayyumu, muna roƙon ka cigaba da taimakon bayinka, ka nuna mana ranar da zalunci da munafukai zasu tozarta.

Post a Comment

0 Comments