Gwamnan Jihar Kano ya nuna damuwarshi akan yacce hukumar Hizba take gudanar da ayyukanta

Gwamnan Jihar Kano ya nuna damuwarshi akan yacce hukumar Hizba take gudanar da ayyukanta 



Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan salon da hukumar Hisba ke bi wajen yaƙi da masu aikata baɗala a jihar.

Yayin da yake jawabi a wani taro da ya yi da limaman Kano a gidan gwamnatin jihar, gwamnan ya ce Hisbah, hukuma ce mai albarka da aka ɗauketa da martaba, aka kuma damƙata a hannun bayin Allah da ake ganin za su iya jagorantarta.

''Mun ɗora musu amanar al'ummar jihar Kano mazansu da matansu, sannan da amanarmu, mu a matsayinmu na shagabanni'', in ji gwamnan.

Abba Gida-gida ya ce ma'anar yin hukumar Hisbah shi ne ta yi abin da yake daidai wajen kawar da ɓarna sannan a bai wa gwamnati shawara.

Amma saɓanin haka, gwamnan ya ce sai hukumar ta ɓuge da aikata wasu abubuwa da ba su dace ba.

Gwamnan ya ce ya ga wani bidiyo da ya tayar masa da hankali, na yadda ma'aikatan hukumar ke kama waɗanda suke zargi da aikata laifi.

''Na ga wani bidiyo, inda ma'aikatan hukumar suka je wurin wasu matasa da ake zargi da aikata laifi, amma yadda aka ɗebo su ana dukansu da gora, suna gudu ana bin su da gora ana taɗe kafafunsu, ana ɗebo su kamar awaki a jefa su cikin mota, Allah ya kiyaye in kashin bayan wani ya karye, ya gama yawo har abada, wannan kuskure ne babba'', in ji gwamnan na Kano.

''Ka rungume matashiya ko matashi ka jefa shi kamar akuya cikin mota, wannan sam bai daidai ba ne''.

''Na ga wani bidiyo inda aka je ɗakunan ɗaliban jami'ar Bayero, har ɗakunansu ana duka ana rungumo su ana jifansu cikin mota, haƙiƙa wannan batu akwai gyara''.

Gwamnan ya ƙara da cewa dole ne hukumar ta sake salo a daburunta na yaƙi da baɗala a jihar, saboda a cewarsa an saka hukumar Hisba ne don ta yi wa addinin musulunci hidima, amma idan ta bi wannan hanya, ba za a samu gyaran da ake so ba, domin waɗanda ake ƙoƙarin su gyarun, sai su kangare.

''Allah ya kiyaye idan waɗannan yara suka kangare mana to ba mu son halin da jiharmu za ta shiga ba''.

Abba Kabir ya ce abin da ya kamata hukumar ta riƙa yi shi ne ta riƙa fita tare da 'yan sanda da 'yan sibil difen da jami'an DSS wuraren da ake aikata baɗalar a kamo su a kai su ga hukuma don a gurfanar da su a gaban kotu, ba tare da cutar da su ba.

''Allah ba ya son tazarci, kuma duk zunubin da mutum ke yi Allah ba ya son a tozarta shi, kun fi ni sanin haka'', kamar yadda ya shaida wa limaman.

''In dai za ku rika hawa mumbari kuna wa'azi da faɗakarwa, insha Allahu za a samu sauyi a ɓangaren tarbiyyar matasanmu'', in ji shi.

Gwamnan ya kuma ce lallami da jan hankali cikin lumana shi ne abin da zai sa fitinannen mutum ya yi nadama kan munanan ayyukan da yake aiwatarwa

Post a Comment

0 Comments