Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen-hula 80 a sabbin hare-hare da ta kai Gaza — Falasɗinu

 Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen-hula 80 a sabbin hare-hare da ta kai Gaza — Falasɗinu

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 80 sannan suka jikkata wasu a hare-haren tsakar dare da suka kai a gidaje da gine-ginen gwamnati a Gaza, a cewar kafofin watsa labaran Falasɗinu da hukumomi.

Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa (WAFA) ya ce Isra'ila tana ci gaba da kai hare-hare babu ƙaƙƙautawa a yankuna daban-daban, ciki har da sansanin ƴan gudun hijira na Nusairat da Birnin Gaza.

Sojoji sun jefa bama-bamai a gidajen da ke Titin Al Jala, inda ɓaraguzan gine-gine suka danne jama'a. Sun rusa wani gini mai hawa bakwai kusa da Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza, inda Falasɗinawan da suka rasa gidajensu suke samun mafaka, abin da ya kai ga mutuwar gomman mutane da jikkatar wasu.

Ma'aikatan agaji sun zaƙulo gawawwaki biyar na Falasɗinawa daga ɓaraguzan gine-gine, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Kazalika Falasɗinawa akalla biyar sun mutu yayin da dama suka jikkata lokacin da Isra'ila ta kai hari a wani gida da ke Tuffah a Birnin Gaza.

A yankin Nasr, sojojin Isra'ila sun kashe mutane da dama lokacin da suka buɗe wuta a wani gida, a cewar ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza. Daga bisani sun kai hari a sansanin ƴan gudun hijira na Nusairat, inda suka kashe fararen-hula aƙalla 36.

Post a Comment

0 Comments