Jami'an tsaron Turkiyya sun kama wasu da ake zargi da tattara wa Isra'ila bayanan sirri

Jami'an tsaron Turkiyya sun kama wasu da ake zargi da tattara wa Isra'ila bayanan sirri


Wani jami'i da ke sa ido kan masu manyan laifuka mai zaman kansa na daga cikin mutanen bakwai da aka kama a farmakan haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Leƙen Asirin Turkiyya da ƴan sandan Istanbul.

Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya (MIT) da ƴan sandan Istanbul sun kama mutane bakwai da ake zargi da sayar da bayanan sirri ga hukumar leƙen asirin Isra'ila (Mossad).

A ranar Talata, majiyoyin tsaro da suka nemi a É“oye sunansu, sun bayyana cewar É—aya daga cikin waÉ—anda ake zargi É—in tsohon ma'aikacin gwamnati ne kuma É—an sandan kama masu aikata manyan laifuka mai zaman kansa.

MIT ta sanar da cewa Hamza Turhan Ayberk na karɓar kuɗi inda yake aika wa hukumar leƙen asirin Isra'ila bayanan sirri.

Majiyoyin sun kuma ce Mossad ta tuntuɓi Ayberk ta hanyar wata ma'aikaciya mai suna "Victoria".

An samu labarin cewa Ayberk ya kafa wata ƙungiya da ta haɗa da ma'aikatan gwamnati da ke samar da bayanan sirri ga Mossad. Ya tattara bayanai game da ɗaiɗaikun mutane ƴan Gabas ta Tsakiya da kamfanoni da ke Turkiyya, kuma bisa umarnin da yake samu daga waje.

Hanyar sadarwa ta sirri

Mossad ta horar da Ayberk a Belgrad a 2019. Majiyoyin sun bayyana cewa hukumar leƙen asirin Isra'ila ta fara aiki da shi wajen ƙananan ayyuka.

Yana amfani da manhajojin sadarwa na sirri ƙarƙashin sanya idanu da umarnin Mossad, kuma yana karɓar kuɗaɗe ta hanyar kuɗin kirifto wanda hakan zai sanya ba a sanya karɓa a hukumance ba.

Haka zalika, baya ga fitar da bayanan sirri, Ayberk na shiga ayyukan leƙen asiri da yin barazana.

Yana aika wa Mossad wuraren da jama'ar da yake bibiya suke ta hanyar amfani da na'urori da yake É—aura wa Æ´an ta'addar Daesh da aka kama a farmakai daban-daban.

A gefe guda, Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya Ali Yerlikaya ya ce a ranar Talatar nan an kama wasu da ake zargin Æ´an ta'adda na Daesh ne su 51.

A sanarwar da Yerlikaya ya fitar ta shafin X ya bayyana cewa ƴan sanda sun kai samame a faɗin Turkiyya ƙarƙashin jagorancin sashen leƙen asiri da yaƙi da ta'addanci.

A yayin farmakin, wanda aka kai a lokaci guda a garuruwa daban-daban, Æ´an sanda sun kama mutane 12 da ake zargi da yi wa Daesh aiki a Istanbul. An kama wasu 17 a sauran garuruwan Turkiyya da suka haÉ—a da Adana, Balikesir da Antalya.

Yerlikaya ya ce "Za mu ci gaba da tabbatar da ƙudurinmu, tare da addu'o'i da goyon bayanku har sai mun kassara ɗan ta'adda na ƙarshe, don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasarmu."

Turkiyya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya na farko da suka ayyana Daesh a matsayin ƙungiyar ta'adda. Tun wancan lokacin ƙungiyar ta fara kai hare-hare a cikin ƙasar, inda ta kashe sama da mutane 300 da jikkata wasu ɗaruruwa a hare-haren ƙunar-baƙin-wake aƙalla 10, harin bam bakwai da hare-haren bindiga huɗu da suka kai a ƙasar.

Post a Comment

0 Comments