Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mata masu ciki da ƙananan yara 36

 Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mata masu ciki da ƙananan yara 36 a sabbin hare-haren da suka kai Gaza

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-hare a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa fararen-hula aƙalla 36, gaibinsu ƙananan yara da mata masu ciki, a cewar wata sanar da hukumomn Falasɗinu suka fitar.

"Sojojin mamaya na Isra'ila sun kai harin bama-bamai a gidan iyalan al Tabatibi da ke yammacin sansanin ƴan gudun hijira na al Jadid a Nuseirat (a tsakiyar Zirin Gaza), inda suka kashe Falasɗinawa 36, galibinsu ƙananan yara da mata masu ciki," in ji sanarwar.

Sojojin sun kai hari kan gidaje aƙalla 12 na fararen-hula a Gaza, a cewar sanarwar.

Ta ƙara da cewa, "Muna ɗora alhakin ƙaruwar kisan ƙare-dangi da ake yi wa fararen-hula kan gwamnatin Amurka, da manyan ƙasashen duniya da Isra'ila the international. Su ne kanwa uwar gami na waɗannan laifukan yaƙi da ake aikatawa."

Post a Comment

0 Comments