Daga Abubakar S. Sabiu
Ranar Mata ta Duniya, ta samo asali ne daga ƙungiyar ƙwadago don neman ta kasance cikin ranakun da majalisar Dinkin Duniya ta san da su a ko wace shekara.
An kuma kafa ta a shekarar 1908, lokacin da mata 15,000 suka gaudanar da gangami a fadin birnin New York suna neman a rage musu yawaan lokutan aiki, da albashi mai kyau, da kuma ba su 'yancin kaɗa kuri'a.
Shekara guda bayan haka ne jam'iyar Socialist ta Amurka ce ta ayyana Ranar Mata ta Duniya ta farko.
Shawarar mayar da ranar ta kasance ta duniya baki ɗaya ta samu ne daga wata mata mai suna Clara Zetkin kamar yadda kuka ga hotonta a ɗofane a sama.
Ta bullo da shawarar ne a shekarar 1910 a wani babban taron ƙasa da ƙasa kan mata a birnin Copenhagen.
Mata 100 ne suka halarci taron daa ƙasashe 17, kuma suka amince da shawararta nan take.
An fara gudanar da bikin ne a shekarar 1911, a kasashen Austria, da Germany da kuma Switzerland.
A shekarar 1975 ne aka tabbatar da bikin ranar a hukumance, lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara bikin wannan rana.
Taken bikin na fako da Majalisar Dinkin Duniyar ta tsayar a shekarar 1996 shi ne "Bikin tuna baya, tsara rayuwa ta gaba."
Ranar Mata ta Duniya ta zama ranar bikin duba halin da mata ke cikin a tsakanin al'umma, a fannonin siyasa, da tattalin arziki, yayin da a tushen siyasar hakan na nufin yajin aiki, kuma a kan shirya gudanar da gangami don faɗakarwa game da cigaba da nuna wariya
Yaushe ne ranar mata ta duniya?
Ranar 8 ga watan Maris ne Ranar Mata ta Duniya da Clara ta bullo da shawara a kai ba ta da takamaimen rana da aka tsayar.
Ba ta kasance a hukumance ba har sai a lokacin wata zanga-zangar lokacin yaƙi a shekarar 1917 lokacin da matan ƙasar Russia suka buƙaci ''biredi da zaman lafiya'' - kana kwanaki hudu da fara yajin aikin matan, aka tilasta wa shugaban ya sauka daga mukaminsa kana gwamnati ta amince wa mata samun 'yancin kada kuri'a.
Ranar Lahadi 23 ga watan Fabrairu ne da matan suka fara gudanar da yajin aikin kan tsarin kalandar kwanan wata ta Julian da kasar Russia ke amfani da ita a wancan lokacin.
A yanzu wannan rana a kan tsarin kalandar Gregorian ta kasance ranar 8 ga watan Maris.
0 Comments