Kwamitin Tsaro na MDD zai kaɗa ƙuri'a kan tsagaita wuta a Sudan gabanin watan Ramadan

Kwamitin Tsaro na MDD zai kaɗa ƙuri'a kan tsagaita wuta a Sudan gabanin watan Ramadan


Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga bangarorin biyu da su mutunta darajar watan Ramadan.


Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kaɗa ƙuri’a a ranar Juma’a kan yin kira da a tsagaita wuta a Sudan, a daidai lokacin da za a fara azumin watan Ramadan a mako mai zuwa, yayin da lamura ke ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, daftarin ƙudurin da aka shirya zai yi kira ga dukkan ɓangarorin da su ɗauki matakin dakatar da rikicin ba tare da ɓata lokaci ba kafin watan Ramadan, lokacin da ya kamata ya zama na ibdar azumi da addu'a da tunani ga Musulman duniya.

Har ila yau, ta yi kira ga ɓangarorin da ke faɗa da juna da su ba da damar kai agajin jinƙai ba tare da wata tangarda ba ta kan iyakoki da kuma filin daga.

A zaman da kwamitin sulhun ya yi a ranar Alhamis, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga dukkan bangarorin Sudan da su mutunta darajar watan Ramadan ta hanyar dakatar da yaƙi a cikin watan mai alfarma.

Ya ƙara da cewa, "Dole ne tsagaita wuta ta haɗa da daina ɓrin wuta a duk faɗin ƙasar, tare da samar da tabbatacciyar hanya wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa ga al'ummar Sudan."

Post a Comment

0 Comments