Pastor Yohanna Y D Buru Ya kai gudummawar geron azumi ga mabuƙata na musamman

Pastor Yohanna Y D Buru Ya kai gudummawar geron azumi ga mabuƙata na musamman

Pastor Yohanna Y D Buru Yayin da yake Raba kayan gudummawar geron azumi ga mabuƙata na musamman


Babban Pastor a Najeriya, Pastor Yohanna Y D Buru Ya kai gudummawar geron azumi ga mabuƙata na musamman dake kano road anan garin kaduna.

A yau lahadi pastor ya kai gudummawar ga Almajirai/Nakasassu dake zaune a kano road anan garin kaduna domin shirin azumin watan Ramadan da ake sa ran shigarsa gobe litinin.

A yayin bayar da wannan gudummawar na geron azumi pastor yayi addu'ar Allah yasa a fara azumin watan Ramadan lafiya kuma a gama lafiya, Ya buƙaci musulmi suyi amfani da wannan watan na Ramadan gurin addu'oi ga halin kunci da azzaluman shuwagabanni suka sanyamu ciki a wannan kasa.


Post a Comment

0 Comments