Ramadan: Shaikh Zakzaky ya yi rabon abinci ga mabuƙata

Ramadan: Shaikh Zakzaky ya yi rabon abinci ga mabuƙata

Daga Ammar Muhammad Rajab

Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky kamar yadda ya saba a duk shekara a lokacin watan azumi na Ramadana, a bana ma ya yi rabon abinci ga mabuƙata a Zariya da wasu garuruwa. 

Rabon kayan abincin ya soma gudana ne da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Laraba 13 ga watan Maris ɗin 2024 daidai da 3 ga Ramadana, 1445. 

Kayayyakin abincin ya haɗa da; gero, masara, sikari, shinkafa da sauran su. 


Shaikh Badamasi Yaqoub, ɗan uwa ga Shaikh Zakzaky shi ne wanda ya jagoranci raba kayan abincin. A yayin rabawar ya shaidawa manema labarai cewa; "wannan hidima na Malam Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky ne wanda ya saba yi duk shekara. Kuma ya soma wannan abin tun kafin abin da ya same shi a 2015 da sojoji suka afka masa a gidansa. Kuma ko da hakan ya faru bai tsaya ba ya ba mu umurnin mu ci gaba da rabawa ba tare da an fasa ba. Kuma tun daga wannan lokacin kowacce shekara muna yi, kuma alhamdulillah kamar yadda kuke gani mun soma yi a bana", ya jaddada. 

Ya tabbatar da cewa mafi aksarin abincin da ake rabawa ba almajiransa bane ke amfana, inda ya ce; "kusan duka kayan abincin nan mutanen gari ake rabawa. Za ku ga harda waɗanda ba ma sunayensu suna yi mana tururuwa a gida, kuma haka nan akan san yadda ake yi suma a ba su na su kason", in ji shi. 

Shehin Malamin ya tabbatar da cewa Shaikh Zakzaky ya kwashe fiye da shekaru 20 yana raba kayan abincin ga mabuƙata a lokacin azumin watan Ramadana. Kuma rabon kayan abincin ana faɗaɗawa zuwa wasu garuruwan dake faɗin Nijeriya. 

Waɗanda suka amfana da wannan kayan abinci, sun bayyanawa manema labarai farin cikinsu. Tare da addu'a ga Shehin Malamin. 

Muhammad daga Gyallesu, ɗaya daga cikin wanda ya amfana da tallafin, ya bayyana cewa yana daga cikin masu amfana da wannan tallafin na tsawon shekaru; "muna godiya, Allah ya saka wa su Malam Zakzaky da alheri. Al'umma na cikin mawuyacin hali amma wannan tallafi daga wannan Bawan Allah yana taimakawa sosan gaske", in ji shi. 

Auwalu daga Sabon Garin Zariya, a yayin da yake bayyana jinɗaɗinsa dangane da tallafin da ya samu a bana, ya bayyanawa cewa; "Ni direba ne, amma duk shekara ana kirana ina ɗauka. Kuma ina jinɗaɗi ina ƙaruwa. Kuma ma waɗanda muke tare da su suna ƙaruwa. Ba abin da za mu ce sai dai Allah ya saka da alherinsa". 

Da yawan waɗanda suka amfana da tallafin abincin sun fito ne daga sassa daban-daban na garin Zariya da kewaye; wanda ya haɗa da cikin garin Zariya, Sabon Gari, Samaru, Bomo da sauran su.

Post a Comment

0 Comments