Rundunar sojin Nijeriya tayi nasarar gano mutum takwas masu hannu wajen kisan dakarunta a Delta
Rundunar sojin Nijeriya na neman mutum takwas ruwa-a-jallo kan kisan dakarunta a Delta
Shugaba Tinubu ya bai wa hedkwatar tsaro da shugaban rundunar tsaron Nijeriya "cikakken iko" na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan sojojin.
Sojojin Nijeriya ta sha alwashin hukunta duk mutumin da ta samu da hannu a kisan dakarunta a ƙauyen Okuama na jihar Delta.
Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta fitar da hotunan wasu mutane da take nema ruwa-a-jallo bisa zargin kisan dakarunta goma sha bakwai a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.
Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, kwana guda bayan an yi wa sojojin jana'izar ban-girma a Abuja, babban birnin ƙasar.
Mutanen takwas, ciki har da mace, su ne Akevwru Daniel Omotegbono wanda aka fi sani da suna Amagbem; Prof. Ekpekpo Arthur, Andaowei Dennis Bakriri da Igoli Ebi.
Sauran su ne Akata Malawa David, Sinclair Oliki, Clement Ikolo Oghenerukevwe da kuma Reuben Baru.
An kashe sojojin ne yayin da suka kai ɗauki ƙauyen na Okuma inda wasu al'ummomi suke rikicin ƙabilanci.
Kusan mako biyu kenan Shugaba Tinubu ya bai wa hedkwatar tsaro da shugaban rundunar tsaron Nijeriya "cikakken iko" na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan sojojin.
Shugaban na Nijeriya ya ce "matsorata" ne suka yi wannan ɗanyen-aiki, yana mai ƙarawa da cewa hakan ba zai sa dakarun ƙasar su karaya wajen wanzar da tsaro ba.
Shugaba Tinubu ya ce "sojojinmu su ne ginshiƙin gina ƙasarmu. Duk wani hari da aka kai musu, hari ne a kan ƙasarmu kai-tsaye. Ba za mu amince da wannan ƙeta ba."
'Ɗaukar nauyin karatu'
Ranar Laraba Shugaban Nijeriya Tinubi ya jagoranci jana'izar ban-girma ga sojojin a Maƙabartar Soji ta Ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya jaddada ta'aziyyarsa ga iyalan sojojin, yana mai jinjina wa dakarun bisa irin sadaukarwar da suka yi domin wanzar da zaman lafiya a Nijeriya.
"Gwamnatin tarayya za ta ɗauki nauyin karatun ƴaƴan dukkan sojojin Nijeriya da aka kashe a Okuama na Jihar Delta har zuwa matakin jami'a, ciki har da waɗanda ake da cikinsu," in ji wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar.
Kazalika Shugaba Tinubu ya umarci hukumomi su tabbatar sun biya iyalan sojojin dukkan kuɗaɗen da suka kamata a ba su cikin kwana 90.
Haka kuma shugaban ƙasar ya ce gwamnatin tarayya za ta bayar da gida ga iyalan kowane soja da aka kashe a ko ina suke so a faɗin Nijeriya.
An karrama manyan sojojin da lambar yabo ta Members of the Order of Nigeria (MON), yayin da aka bai wa ƙanana daga cikinsu lambar yabo ta Officers of the Federal Republic.
0 Comments