Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaza ya kusa 33,000

 Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaza ya kusa 33,000


Daga Mahadi Umar kaita 

Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a Falasɗinu ya ƙaru zuwa 32,975 tun daga Oktobar bara, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta fitar da sanarwar a lokacin da aka shiga rana ta 180.

Hare-haren da ake kaiwa a Gazar ya yi sanadin mutum 75,577 sun samu rauni, kamar yadda ta ƙara da cewa.

Ma’aikatar ta ce a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Isra’ilar ta kashe mutum 59 da raunata 83 a faɗin Gaza.

Allah ya kawoma Al'ummar Falasdinu dauki 💔🙌

Post a Comment

0 Comments