An gurfanar da jami'in Binance a gaban kotun Nijeriya

An gurfanar da jami'in Binance a gaban kotun Nijeriya


Ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma Tigran Gambaryan ya je kotun da misalin ƙarfe 9:15 na safiyar Alhamis ɗin nan, amma abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla bai gurfana a gaban kotun ba saboda an ce ya tsere daga Nijeriya.


 Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da kamfanin Binance da manyan jagoririnsa biyu; Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da ya tsere, a gaban kotu.

An gurfanar da Tigran Gambaryan a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Alhamis ƙarƙashin mai shari’a Emeka Nwite.

Tigran Gambaryan ya je kotun da misalin ƙarfe 9:15 na safiyar Alhamis, amma abokin aikinsa Anjarwalla bai zo ba sabon an ce ya gudu daga ƙasar.

Har yanzu kotunan na hutun Easter amma bayanai sun ce alƙalin kotun bai je hutun ba saboda ya saurari wannan ƙara mai matuƙar muhimmanci.

Ana tuhumar mutanen biyu da laifuka biyar na halatta kuɗaɗen haramun da gudanar da kasuwanci a Nijeriya ba tare da lasisi ba.

A watan jiya ne jami'an tsaron Nijeriya suka tsare Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla.

Shugabannin Binance ɗin sun je Nijeriya ne bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rufe manhajar.

An tsare shugabannin na Binance ne saboda sun kasa ba da gamsassun bayanai kan yadda manhajar take hada-hadar kuɗi a Nijeriya.

A wancan lokacin, wata majiya a fadar shugaban Nijeriya ta tabbatar wa TRT Afrika cewa manyan batutuwa uku ne suka damu gwamnatin ƙasar kan hada-hadar Binance a ƙasar.

Na ɗaya, kamfanın bai yi rajista da hukumomin ƙasar ba, sannan gwamnati ba ta samun haraji daga ɗimbin ribar da Binance ke samu daga hada-hadar da yake yi a ƙasar, matakin da ke yin illa ga tattalin arzikinta.

Na biyu, babu gamsassun bayanai kan adadin ƴan Nijeriya da ke hulɗa da Binance da kuma yawan kuɗin da ake hada-hadar su.

Na uku, gwamnatin Nijeriya na zargi cewa masu aikata laifukan da suka shafi harkokin kuɗi da masu neman kuɗin fansa suna amfani da manhajar wajen musayar kuɗaɗe ba tare da wata kafa ta iya bibiyarsu don gano abubuwan da suke yi ba.

Post a Comment

0 Comments