An sake dage Shari'ar ƴan uwa Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky 60 da ake tsare da su a gidan yarin Kuje a Abuja

An sake dage Shari'ar ƴan uwa Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky 60 da ake tsare da su a gidan yarin Kuje a Abuja



Daga Ibrahim s Umar Katsina 

 An sake dage Shari'ar ƴan uwa Almajiran Sayyed Ibraheem Zakzaky (H) 60 da ake tsare da su a gidan yarin Kuje a Abuja, Shari'ar wadda aka tsara cewa za'a zauna a yau Talata 30th April a cikin gidan yarin na Kuje kamar yadda aka saba.

 An ɗage wannan shari'ar ba tare da ma an zo zaman kotun na yau ba, sannan ba'a ayyana wata sabuwar ranar da za'a dawo don ci gaba da Shari'ah ɗin ba.

 Dama a baya mun bayyana cewa " a duk sadda aka sanya zaman kotun nan mukan zauna cikin zullumi ne har sai mun ga yiwuwar zaman" saboda wannan Azzalumin Alƙalin ya saba duk sadda ya sa za'a zauna don yin shari'ar sai ranar ta zo sai ya ce an fasa.

 Allah ya ƙara ma ƴan uwa dauriyar wannan yanayi, ya basu ikon cinye wannan jarabawar, Allah ya gaggauta turmuza hancin Azzalumai.

Post a Comment

0 Comments