An samu rabuwar kawuna tsakanin mambobin majalisar ministocin haramtacciyar Isra'ila kan batun kaima Iran hari.
Bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai wa HKI a ranar Asabar da ba a taba ganin irinsa ba, an samu mabambantan ra'ayoyi a yayin taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Lahadi a hedikwatar ma'aikatar tsaro da ke Tel Aviv, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.
''Akwai yarjejeniya kan wajibcin mayar da martani kan harin Iran, amma an samu rarrabuwar kawuna da ya shafi ma'auni da kuma lokacin da za a mayar da martani, ba tare da an bijire wa matsin lambar Amurka da na kasashen duniya ba," kamar yadda Tashar talabijin ta Isra'ila 12 ta ruwaito.
A safiyar ranar Lahadin da ta wuce ne, gidan yada labarai na Isra’ila KAN ya fitar da sanarwar cewa ''cikin mintunan karshe ne aka soke matakin mayar da martani kan harin da Iran ta kai'' bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Joe Biden.
0 Comments