An samu rahoton fashewar wasu abubuwa a Lardin Isfahan dake tsakiyar ƙasar Iran a yau Juma'a

 An samu rahoton fashewar wasu abubuwa a Lardin Isfahan dake tsakiyar ƙasar Iran a yau Juma'a 


Daga Mahadi Umar kaita 

Kafafen watsa labaran Iran sun bayar da rahotannin fashewar wasu abubuwa a lardin Isfahan da ke tsakiyar ƙasar ranar Juma'a, a yayin da kafofin watsa labaran Amurka suka ambato jami'an gwamnatin ƙasar suna cewa Isra'ila ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan abokiyar gabarta.

Iran ta sanya na'urorinta da ke kare sararin samaniya cikin shirin ko-ta-kwana a birane da dama bayan kafar watsa labaran gwamnatin ƙasar ta ce an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a kusa da birnin Isfahan.

A baya, Isra'ila ta sha alwashin mayar da martani bayan Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kai-tsaye a cikin yankinta.

Ta ɗauki matakin ne bayan Isra'ila ta kai hari a ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, babban birnin Syria inda ta kashe zaratan sojojinta bakwai, ciki har da janar-janar biyu.


Ku kasance da Muryar Labarai domin Jin Labarai Abubuwan dake faruwa a gabas ta tsakiya.

Post a Comment

0 Comments