Dasau lafiyarta lau babu wata rashin lafiyar da takeyi lokaci guda ta rasu

 Dasau lafiyarta lau babu wata rashin lafiyar da takeyi lokaci guda ta rasu


Daga Hafsat Abdullahi 

Allah Ya yi wa fitacciyar tauraruwar finafinan Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da Saratu Daso rasuwa.

Ta rasu ne ranar Talata a birnin Kano da ke arewacin Nijeriya.

Shugaban hukumar tace finafinai na jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha ya ce Daso ta rasu ne "bayan kwanciya barci da ta yi bayan gama sahoor."

Danginta sun ce za a yi jana'izarta bayan la'asar.

Daso tana cikin taurarin finafinan Kannywood da aka daɗe ana damawa da su.

Baya ga harkar fim, marigayiyar tana gudanar da gidauniya ta musamman wadda ke taimaka wa marayu da marasa galihu.

Makusancin marigayiya Saratu Gidado yace marigayiyar lafiyarta lau babu wata rashin lafiyar da take yi, lokaci guda ta rasu a yau Talata. 

Muna mata Addu'ar Allah ya jikanta da Rahama, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani.

Post a Comment

0 Comments