Dole ne mata su daukeni a matsayin 'yar uwa, domin ni mace ce" - Bobrisky

 Dole ne mata su daukeni a matsayin  'yar uwa, domin ni mace ce" - Bobrisky



Shahararren Dan  Najeriya Okuneye Idris Olanrewaju, Wanda  aka fi sani da Bobrisky ya bayyana kanshia a matsayin mace yayin da ya bayyana cewa mata ba su da wani zabi illa amincewa da shi a matsayin ‘yan uwarsu domin shi mace ce ba namiji ba.

Wannan ikirari ya zo ne a  cikin wani sabon rubutu daya fitar mai taken: “Mata ba su da zabi. Dole ne su yarda da ni a matsayin ɓangare na 'yan uwantaka. Ni mace ce." "Dole ne mata su yarda da ni a matsayin 'yar uwarsu mace, ni mace ce" 

Wannan sanarwar ta biyo bayan nasarar da Bobrisky ya samu a matsayin mafi kyawun sutura a rukunin mata. Dangane da lashe kyautar duk da cewa ba mace ce ta ilimin halitta ba, da yawa daga cikin taurarin fina-finan Nollywood da 'yan Najeriya da suka damu sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan lamari mai ban mamaki.

A cikin sukar da ya biyo bayan kyautar, Bobrisky, a wani sabon bayani da ya fitar, ya bayyana karara cewa yana bukatar mutunta mata da kowa da kowa kuma bai kamata a rika sukar ta ba saboda ta bayyana kanta a matsayin mace. Ya kara da cewa ya kamata mata su yarda da ita a matsayin ‘yan uwantaka, domin babu wani abin da za su iya sai su yarda tunda ta bayyana mace ce.

Post a Comment

0 Comments