Gwamnan Jihar Katsina ya biya tara don sakin Fursunoni 222 Albarkacin Watan-Ramadan

Gwamnan Jihar Katsina ya biya tara don sakin Fursunoni 222 Albarkacin Watan-Ramadan 


Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Dikko Umaru Radda, ya biya tara don sakin Fursunoni 222 Albarkacin Watan-Ramadan da kuma Bikin Sallah 

A yau 8 ga Afrilu, 2024 a cikin shirinsa na azumin Ramadan da goron-Sallah, Gwamna ya biya tarar fursunoni 222 da ke gidajen gyaran hali daban-daban a fadin jihar Katsina, wadanda ake tsare da su saboda kasa biyan kudin tarar da kotuna daban-daban su ka sanya musu.

Fursunonin da aka ɗauka waɗanda ke da ʙananan laifukan da suka danganci kasuwanci ne da sauran kananan laifuka. An tantance fursunonin da suka samu wannan damar, kuma an ba da shawara ga gwamnatin jihar domin ta shiga tsakani don biyan kudaden da su ka yi sanadiyar rike su a gidajen gyaran hali.

Matakin da gwamnatin jihar ta dauka zai rage cunkoso a gidajen gyaran hali sannan kuma zai baiwa fursunonin da aka sako damar yin bukukuwan Sallah tare da ‘yan uwansu.

Sa Hannu;

Fadila Muhammad Dikko 

Kwamishinyar Shari'ah ta Jihar Katsina.

Isah Miqdad, 

SSA Digital Media to Katsina State Governor.

8/4/2024

Post a Comment

0 Comments