Iran ta fito da 'makamai masu linzami fiye da 100' don kai wa Isra'ila hari

Iran ta fito da 'makamai masu linzami fiye da 100' don kai wa Isra'ila hari



Iran ta fito da makamai masu linzami don kai harin ramuwar gayya bayan Isra'ila ta kai hari a ofishin jakadancin Iran da ke Syria wanda ya yi sanadin mutuwar zaratan sojojinta bakwai, ciki har da janar-janar biyu, a cewar gidan talbijin na ABC News.

Gidan talbijin na ABC News ya ambato wasu majiyoyi a ma'aikatar tsaron Amurka ranar Juma'a suna cewa gwamnatin da ke Tehran ta shirya makamai masu linzami sama da É—ari don yin ramuwar gayya kan Isra'ila./Hoto: Reuters

A yayin da ake zaman ɗar-ɗar tsakanin Isra'ila da Iran, bayanai sun ce mahukunta a Tehran sun "fito da makamai masu linzami sama da ɗari ɗaya waɗanda ke da gudun gaske domin yiwuwar kai hari" kan Isra'ila, kusan mako biyu bayan Isra'ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus inda ta kashe zaratan sojoji bakwai na ƙasar, ciki har da janar-janar guda biyu.


Gidan talbijin na ABC News ya ambato wasu majiyoyi a ma'aikatar tsaron Amurka ranar Juma'a suna cewa gwamnatin da ke Tehran ta shirya makamai masu linzami sama da ɗari don yin ramuwar gayya amma Amurka ta tura ƙarin kayan yaƙi yankin, ciki har da jiragen ruwa da na sama na yaƙi.


A halin da ake ciki Amurka ta aika makaman da ke lalata jiragen ruwan yaƙi zuwa yankin gabas na Bahar Rum da nufin kare Isra'ila, in ji rahoton ABC News..

Post a Comment

0 Comments