Iran ta kaddamar da harin ramuwar gayya kan yankunan da ta mamaye a matsayin mayar da martani

Iran ta kaddamar da harin ramuwar gayya kan yankunan da ta mamaye a matsayin mayar da martani.
✍️ Mahadi Umar kaita

Rahotanni daga kasar Iran na cewa, kasar Iran ta kaddamar da harin ramuwar gayya kan yankunan da ta mamaye a matsayin mayar da martani ga harin ta'addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan sashin karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Damascus na kasar Siriya a ranar 1 ga watan Afrilu.

An kaddamar da hare-haren ne a yau Asabar Sha ukwu ga watan nan da muke ciki, inda wasu rahotanni ke cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kaddamar da hare-hare da jiragen yaki marasa matuka zuwa yankunan da ta mamaye. 

Har yanzu Iran ba ta amince da kai harin ramuwar gayya ba a hukumance. 

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, har yanzu Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta harba makamai masu linzami a matakin da take dauka na ramuwar gayya kan gwamnatin mamaya ba, yana mai cewa akwai yiyuwar ta auka wa birnin Haifa data mamaye a gabar tekun.

Tashar Talabijin ta 12 ta Isra'ila ta tabbatar da cewa an kai wa gwamnatin kasar hari, tana mai cewa Iran ta harba jiragen yaki marasa matuka zuwa yankunan da ta mamaye

Ku kasance da muryar Labarai domin sanin yacce zata kaya tsakanin Musuluncin Duniya dakuma kafircin duniya.

Muryar Labarai 

Post a Comment

0 Comments