Isra'ila ta yi kuskure kuma dole ne a hukunta haramtacciyar gwamnatin Isra'ila ," in ji Ayatullah Khamenei

 Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce dole ne a hukunta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila 


Daga Mahadi Umar kaita 

Yace hakan ne saboda mummunan harin da ta kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus babban birnin kasar Siriya. 

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a babban masallacin Juma'a na Imam Khumaini da ke birnin Tehran babban birnin kasar Iran a ranar Larabar da ta gabata, bayan da ya jagoranci sallar idin layya, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan. 

Jagoran ya yi ishara da harin makami mai linzami da Isra'ila ta kai kan sashin karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus babban birnin kasar Siriya a ranar 1 ga watan Afrilu.

 Ayatullah Khamenei ya ce: Muguwar gwamnatin sahyoniyawan ta sake yin wani kuskure... kuma wannan shi ne harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Siriya. 

An dauki ofishin jakadancin da ofisoshin diflomasiyya a kowace kasa a matsayin yankin kasar.  Lokacin da suka kai wa ofishin jakadancinmu hari, yana nufin sun kai wa kasarmu hari." 

"Muguwar gwamnatin ta yi kuskure kuma dole ne a hukunta ta kuma za a hukunta ta," in ji Jagoran.

 Harin na Isra'ila ya kashe wasu manyan jami'an sojan Iran biyu da ke aikin ba da shawara a Siriya da kuma wasu jami'ansu biyar. Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa, Birgediya Janar Mohammad Reza Zahedi kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) da mataimakinsa Janar Mohammad Hadi Haji Rahimi na daga cikin shahidai bakwai da suka yi shahada.

Zuwa kawo maku wannan rahoton, Rahotanni sun tabbatar cewa an ga manyan makamai masu linzami da aka harba daga Yemen suna shawagi a sararin samaniyar Isra'ila. 

Ku biyomu kusha labaarai a Muryar Labarai 

Post a Comment

0 Comments