Shari'ar ƴan uwa Musulmi 60 da ake tsare dasu a kurkukun kuje tsawon shekaru biyar

 Shari'ar ƴan uwa Musulmi 60 da ake tsare dasu a kurkukun kuje tsawon shekaru biyar.

Daga Mahadi Umar kaita 

Tsawon shekaru biyar kenan ana tsare da Yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Zakzaky wadanda aka kama a wajen fafutukar neman yancin shehun malamin a shekarar 2019 a birnin tarayyar Abuja.

Saidai har kawo yanzu ba'a samu zama a kotu ba domin yanke hukunci akan Shari'ar, inda duk lokacin da aka sa zaman Shari'ar nan Yan uwan sukan zauna cikin rashin tabbas har sai anga yiwuwar shi, kasantuwar muguntar alkalin na yin wasa da hankalin Shari'ar cikin dabara.

Mun samu tabbacin cewa Alkali Belgore ya shahara wajen rike wadanda yake gabatar da Shari'a a kan su tsawon shekaru Kuma yaci gaba da tsare su a gidan yari ba tare da an yanke hukunci akan Shari'ar ba.

Idan Allah ya kaimu 30th ga watan Afrilu ne ake sa ran ci gaba da zaman Shari'ar ƴan uwan 60 da ake tsare dasu bisa zalunci na tsawon lokaci.

Muna rokon Yan uwa da su Saka wadannan bayin Allah a cikin addu'ar Allah ya daurasu akan dukkan wani azzalumi.

Post a Comment

0 Comments