Shekaru 31 da daya da da fara shekar da jinanen Almajiran Sheikh Zakzaky

Shekaru 31 da daya da da fara shekar da jinanen Almajiran Sheikh Zakzaky

Duk da yanayin tsanani takurawar jami'an tsaro an fita jerin gwanon

Daga Mahadi Umar kaita 

Ranar 19 Ga Watan Aprilu, Ranar Da Aka Fara afkawa Yan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Zakzaky.

 Ranar 19 Ga watan Aprilu rana ce da aka fara sheÆ™ar da jinanen yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H). Waki'ar wanda ta faru a garin Katsina bayan an fitowa wata Muzaharar lumana domin nuna rashin amincewa da É“atanci GA Annabi da wata Jarida Mallakin gwamnatin Najeriya tayi a lokachin.

 A irin wannan rana yan uwa Musulmi sun fito Muzahara a duk faÉ—in Æ™asar nan domin nuna rashin amincewarsu akan cin zarafin da wannan jaridar tayi ga Manzon Allah (S) inda har yan uwa suka Æ™ona copy na Jaridar a yayin Muzaharar. A ko ina an kammala Muzaharar lafiya amma a Katsina bayan an kammala sai gwamnan Soja na lokacin mai suna Yohanna John Madaki ya fito a kafafen watsa labarai yana cewa "Idan aka Æ™ara Irin wannan zanga-zangar zai tafi har gidan Sheikh YaÆ™oub Yahaya ya kamo shi ya kai shi har filin Polo ya harbe shi".

 Wannan kalaman da John Madaki yayi yasa Sheikh Zakzaky yazo har nan Katsina domin jan kunne ga shi Yohanna John Madaki, sannan kuma ya taya Sheikh Yakubu Yahaya murnar wannan babban matsayi da ake masa barazana da ita na samun Shahada, har Sheikh Zakzaky yake kiran Malam Yakubu Yahaya da gwarzon kare Martabar Manzon Allah (S).

 Bayan Sheikh Zakzaky (H) ya gama jawabin jan kunne ga John Madaki. Sannan ya bada umarni cewa a sake wata Muzaharar ranar Juma'a da zata zo a wanann satin. Wannan yasa hukuma ta shirya sosai domin dirarwa yan uwa da nufin ganin cewa ba ayi wannan Muzaharar ba, ko kuma a lokacin da ake Muzaharar su afkawa Muzaharar. Idar da sallar Juma'a keda wuya sai yan uwa suka hau sahu aka fara Muzahara, a dai-dai wani waje da ake kira Kasuwar Gwangwan sai jami'an tsaron Æ´an sanda suka fara Harbo tiyagas da kuma dukan yan uwa da sanduna.

Kusan a wannan waÆ™i'ar ne aka fara samun Shahidi a wannan Harka da Sheikh Zakzaky yake jagoranta. 

Yau Juma'a 19 GA watan Aprilu yayi daidai da irin ranar Wanda wancan ranar itama ta kama a ranar juma'a ne Kuma 19 ga wata kamar dai yau.

Ga wasu Hotunan abubuwan da suka faru a lokacin 👇

WaÉ—anda aka kama har suka zauna a kurkuku tare da Sheikh yakubu yahaya bayan fitowarsa

Wadanda aka saki tare da Sheikh Zakzaky H a Zariya kafin su wuto Katsina



Almajiran Sheikh Zakzaky kenan cikin shirin fita jerin gwanon a 19 ga watan Afrilu.


Post a Comment

0 Comments