Sojojin Nijeriya sun kashe ƴan ta'adda da yawa a Katsina da Zamfara

Sojojin Nijeriya sun kashe ƴan ta'adda da yawa a Katsina da Zamfara


Daga Hafsat Abdullahi 

Sojojin Nijeriya sun yi ba-ta-kashi da ƴan bindiga a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Faskari da ke Katsina inda suka kashe guda takwas tare da ƙwato bindigogi uku ƙirar-gida, da kakin soji da hatsi mai yawa, a cewar sanarwar.

Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta ce dakarunta da ke yaƙi da ta'addanci a Katsina da Zamfara sun kai jerin samame a maɓoyar ƴan ta'adda inda suka kashe da dama daga cikinsu.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin da safe.

Kazalika ta ce dakarunta sun kama tarin miyagun ƙwayoyi a hannun wasu masu fasa-ƙwauri a jihar Ogun da ke kudancin ƙasar kuma za ta miƙa su ga hukuomin da suka dace.

"A samamen da suka kai Zamfara ranar 29 ga watan Maris, dakarunmu sun yi nasarar far wa maɓoyar gawurtaccen ɗan ta'adda, Hassan Yantagwaye, a ƙaramar hukumar Tsafe.

Yantagwaye da tawagarsa ne suka yi garkuwa da mutane da dama tare ta'addanci a wasu yankuna Arewa Maso Yammacin Nijeriya. Yayin samamen, dakarun sun yi luguden wuta a kan ta'adda bayan sun yi musayar harbe-harbe, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da ƙwace makamai da dama," in ji sanarwar.

Kazalika ranar 30 ga watan Maris, dakarun rundunar sojojin Nijeriya sun yi ba-ta-kashi da ƴan bindiga a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Faskari da ke Katsina.

Post a Comment

0 Comments