Tashe-tashen hankula ya tilastama yan Nijeriya da dama gudun hijira zuwa Nijar
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a cikin ƙasa da mako guda mutum 1,400 ne suka tserewa hare-haren ƴan bindiga daga Najeriya zuwa yankin Maraɗi na jamhuriyar Nijar da ke iyaka da ƙasar.
Hukumar ta ce wannan shi ne adadi mafi yawa da aka ga ƴan gudun hijira a wannan shekarar, lamarin da ke buƙatar agajin gaggawa a yankin.
0 Comments