Turkiyya ta dakatar da cinikayya da Isra'ila sai an tsagaita wuta a Gaza


Turkiyya ta dakatar da cinikayya da Isra'ila sai an tsagaita wuta a Gaza


Rahoton TRT Africa 

Turkiyya ta dakatar da cinikayya da Isra'ila sai an tsagaita wuta a Gaza

Ma'aikatar Cinikayya ta Turkiyya ta dakatar da fitar da kaya 54 zuwa Isra'ila, waɗanda suka haɗa da rodi da gorar-ruwa da baƙin-ƙarfe da mabil da tayil.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bisa yin biyayya ga dokokin ƙasashen duniya da kuma tursasa wa Isra'ila bin dokokin da ta daɗe tana karyawa.

Turkiyya ta sanar da dakatar da cinikayya da Isra'ila a wani mataki na ƙuntata wa Tel Aviv kan luguden wutar da suke yi wa Falasɗinawa wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 33,000 a cikin watanni shida.

Ma'aikatar Cinikayya ta Turkiyya ranar Talata ta bayyana cewa ba za ta janye matakin ba sai Isra'ila ta tsagaita wuta sannan ta bari a shigar da "isassun kayan agaji kuma ba tare da shamaki ba" a yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya.

"Ba za a janye wannan mataki ba sai lokacin da Isra'ila ta tsagaita wuta nan-take kana ta bari a kai kayan agaji cikin Gaza ba tare da wani tarnaƙi ba," in ji wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar.

“Isra'ila tana ci gaba da keta dokokin ƙasashen duniya kuma ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi mata na tsagaita wuta da kuma bari a shiga da kayan agaji ba tare da shamaki ba,” a cewar sanarwar.

Ta ƙara da cewa ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da Babban Zauren Majalisar da Hukumar Kare Hakkin Ɗan'adam ta Majalisar na ranar 26 ga watan Janairu da wani irinsa na Kotun Ƙasa da Ƙasa na ranar 28 ga watan Maris sun zargi Isra'ila da keta dokar hana Kisan Ƙare-Dangi, kuma sun nemi "Isra'ila ta tsagaita wuta".

Sanarwar ta ƙara da cewa dole ne Tel Aviv ya, “haɗa kai cikakke da MDD, kana ya bari a shigar da kayan agaji ga Falasɗinawa da ke Gaza, ciki har da magunguna da masu kula da lafiya da ake buƙata.”

Post a Comment

0 Comments