'Yan kasuwa sun rufe hanyar Katsina zuwa Kaita da motoci akan musgunawar da jami'an tsaro ke masu idan zasu kai kayan masarufi kasuwar Kaita da Dankama


 'Yan kasuwa sun rufe hanyar Katsina zuwa Kaita da motoci akan musgunawar da jami'an tsaro ke masu idan zasu kai kayan masarufi kasuwar Kaita da Dankama




'Yan kasuwar suna zargin jami'an tsaro da amsar kuɗaɗen haram a hannun su duk a lokacin da zasu kai kaya a kasuwanni.

Sun faɗi cewa suna kashe kimanin naira dubu 30 zuwa dubu 100 kuɗin hanya a duk sati idan zasu kai kaya koda kuwa mangwaro ne. 

'Yan kasuwar sun nuna matuƙar baƙin ciki bisa halin da suka tsinci kansu duk da cewa suma 'yan Nigeria ne kuma a cikin ƙasar za su kai kayan. 

Katsina Post ta ruwaito cewa majalisar dokoki tasha tattauna irin wannan matsalar ta musgunawar da jami'an tsaro ke yima yan kasuwar dake shigar da kaya a kasuwanni Kaita, Maiadua, Jibia da sauran garuruwan dake kusa da boda amman ba'a ɗauki mataki ba. 

Ya kuke ganin za'a shawo kan matsalar?

Post a Comment

0 Comments