‘Yan sanda sun yi artabu da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Abuja

‘Yan sanda sun yi artabu da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Abuja.

Daga Hafsat Abdullahi 

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya abuja, ta bankado maboya da hanyoyin da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a cikin tsaunuka da dazukan da ke kewaye da Apo-resettled a Abuja.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan, SP Josephine Adeh, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, “Jami’an ‘yan sandan babban birnin tarayya abuja karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan, CP Benneth Igweh, sun kai farmaki kan tsaunukan da ke kewaye da shiyya ta A da B na Apo-resettlement, a ranar 1 ga Afrilu, 2024. , da misalin karfe 11 na safe, domin daukar wasu matakan tsaro a yankin, domin ana kyautata zaton hanyoyin masu garkuwa da mutane ne da kuma maboyar miyagu.

A cewar sanarwar, Igweh ya bukaci mazauna yankin da su sanya ido tare da kai rahoto ga ‘yan sanda da zarar sunga wani abu da basu yadda dashi ba.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ko a watan Maris rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kona maboyar masu garkuwa da mutane kusa da unguwar Awgbu da ke karamar hukumar Orumba ta Arewa inda ta kwato bindiga kirar AK-47 dauke da harsasai 50.

Post a Comment

0 Comments