Abunda ke faruwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau din nan.

Abunda ke faruwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau din nan.


Da yammacin yau din nan ne muka samu labarin Wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya yi hatsari Amman har yanzu babu tabbacin Hakan domin ba'a samu ganin jirgin nasu ba har yanzu kamar yadda gidan talabijin din kasar Iran ya ruwaito. 

Shugaban kasar Ibrahim Ra'isi ya je Azerbaijan da sanyin safiyar yau din nan don kaddamar da wata madatsar ruwa tare da shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev. Dam din dai shi ne na uku da kasashen biyu suka gina a kan Kogin Aras.

A hanyarsu tasu ta dawowa daga Azerbaijan ne aka samu labarin hadarin nasu Wanda har yanzu ba'ada tabbaci domin ba'a gansu ba Kuma babu wani labai domin masu aikin ceto sun yi ƙoƙarin zuwa wurin, amma rashin yanayi mai kyau ya kawo musu cikas. Rahotanni sun ce an samu ruwan sama da iska mai ƙarfi Wanda yayi sanadiyar yin cikas ga masu ceton.

Shugaban Ma'aikatan Sojojin Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya bayar da umarni ga sojojin ƙasar da su yi amfani da duk wasu hanyoyin da suke da su wurin taimakawa don gano wurin da hatsarin ya faru.

Mu Saka su addu'a 

Mahadi Umar kaita

Imamu Alkaitawiy ✍️

Rahoton TRT Africa Hausa 👇

Wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya yi hatsari a ranar Lahadi, kamar yadda gidan talabijin din kasar Iran ya ruwaito, sai dai gidan talabijin ɗin bai yi ƙarin haske kan halin da shugaban yake ciki ba.

Rahotanni sun ce Ministan Harkokin Wajen Iran Abdollahian shi ma yana cikin jirgin da ke É—auke da Raisi.

Kafar watsa labaran ƙasar ta ce lamarin ya faru ne a kusa da Jolfa, wanda birni ne da ke kan iyaka da Azerbaijan, kilomita 600 daga Tehran babban birnin ƙasar.

Masu aikin ceto sun yi ƙoƙarin zuwa wurin, amma rashin yanayi mai kyau ya kawo musu cikas. Rahotanni sun ce an samu ruwan sama da iska mai ƙarfi.

Raisi ya je Azerbaijan da sanyin safiyar Lahadi don kaddamar da wata madatsar ruwa tare da shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev. Dam din dai shi ne na uku da kasashen biyu suka gina a kan Kogin Aras.

Iran na da jirage masu saukar ungulu da dama, sai dai irn takunkuman da aka saka wa ƙasar, ba ta iya samun kayayyakin gyaran jiragen cikin sauƙi.

Wasu daga cikin jiragen da ake amfani da su a ƙasar tun na zamanin juyin juya halin da aka yi a ƙasar a 1979.

Tuni aka tura masu aikin ceto wurin da ake zargin hatsarin ya faru domin gano wurin da aka yi hatsarin.

Shugaban Ma'aikatan Sojojin Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya bayar da umarni ga sojojin ƙasar da su yi amfani da duk wasu hanyoyin da suke da su wurin taimakawa don gano wurin da hatsarin ya faru.

Tuni aka soma taruwa a wurare da dama na Iran ɗin inda ake yi wa shugaban ƙasar addu'o'i.

Post a Comment

0 Comments