Gwamnatin jihar sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta karɓi yara ƙanana da aka yi safararsu daga jihar zuwa Abuja.
A ranar Talata ne rundunar ƴansandan Abuja ta ce ta kama wata jami’ar ‘yansanda mai muƙamin mataimakiyar sufritanda da wata mata da ake zargin sun sato yaran da shekarunsu ba su fi biyar ba ciki har da jaririya ƴar makonni biyu.
Dr Jabir Sani Maihula kwamishinan lamuran addini na jihar Sokoto shi ne ya bi sawun yaran har zuwa Abuja bayan kwarmata masa matar da aka gani a tashar Sokoto ɗauke da yaran da ake zargi ba nata ba ne.
A cewarsa, ya ga yara guda uku, "babban ta ce min sunanta Asma'u, sannan biyun ƙanana ba sa iya faɗin sunansu."
Dr Maihula ya ce ya sanar da gwamnan jihar Sokoto halin da ake ciki inda kuma ya "tura kwamishinan ƴansanda na jihar domin tabbatar da cewa an kai yaran Sokoto da kuma waɗanda suka kama yaran."
Ya bayyana cewa tun isar yaran jihar, an kasi asibiti ne domin duba lafiyarsu.
0 Comments