Babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya ce kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunar ta'azzarar rikicin

 Babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya ce kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunar ta'azzarar rikicin


Babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya ce kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah gabanin hare-haren da ake sa ran za ta ƙaddamar wani "mummunan lamari ne da ka iya ta'azzara yaƙin da ake yi, kuma zai jawo ɗumbin matsaloli."

Kazalika jami'an Hamas sun yi ikirarin cewa matakin kwashe Falasdinawa daga Rafah zai jawo tsaiko wajen sasantarwar sakin mutanen da ake garkuwa da su.

Sojojin Isra'ila sun fara kwashe mutane da ga yankunan da ke kusa da kan iyakar gabashin Rafah, gabain wani farmaki ta ƙasa da ake sa ran za a kai a birnin Falasɗinun da ke kudancin Gaza a yau.

Duk da ƙaruwar adawa da yake fuskanta daga ƙasashen duniya, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin kai farmaki Rafah, yankin da ke ɗauke da Falasɗinawa fiye da miliyan

Post a Comment

0 Comments