Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci cafke tsohon hafsan sojojin ruwa a Najeriya.
Jaridar Leadership ta ce kotun ta bukaci a kama Vice Admiral Usman Jibrin da wasu mutane biyu kan badakalar makudan kudi har N1.5bn.
Mai Shari'a, Inyang Ekwo shi ya ba da wannan umarni a yau Juma'a 3 ga watan Mayu a Abuja.
Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ita ta gurfanar da mutanen uku a gaban kotu kan almundahana da makudan kudi.
Kotun ta ba da umarnin cafke mutanen bayan karbar korafi mai lamba FHC/ABJ/CR/158/2023 daga lauyan hukumar mai suna Osuobeni Ekoi Akponimisingha.
Lauyan ya gurfanar da Usman Jibrin Oyibe da Adam Imam Yusuf da Burgediya-janar Ishaya Gangum Bauka. Ana zargin mutanen da ba da bayanan karya ga kamfanoni da suke da hannun jari a ciki.
Kamfanonin sun hada da Lahab integrated da Multi Services Limited da Gate Coast Properties International Limited da Ummays Hummayd Energy Ltd.
0 Comments