Batun makomar Iyaayen Annabi tun daga kan Adamu Hauwa'u Abdullahi Amina babu kafiri -Al-Zakzaky

Batun makomar Iyaayen Annabi tun daga kan Adamu Hauwa'u Abdullahi Amina babu kafiri -Al-Zakzaky



Daga Bilya Hamza Dass

Batun Makomar Iyayen Annabi; Shaikh Zakzaky ya rufe zance. “Tun daga kan Adamu da Hauwa'u Har zuwa Abdullahi da Amina Babu Kafiri ko guda ɗaya.” 

“Tun daga Adamu zuwa Manzon Rahama (As) babu kafiri ko guda 1, duk cikar su muminai ne bayin Allah ma'asumai gaba ɗayan su. Idan mutum yaso ya fadi duk abinda yaga dama ruwaya ne idan baka da shi mu muna da shi!

“Shaikh ya ƙara da cewa; Idan baka da shi mu muna da shi, idan kuma baka yarda da namu ba ko ka riƙe kayan ka, yauwa, ka riƙe kayan ka mu riƙe na mu. Kowa da inda yake ɗebo Ilimi. Mu inda muka samo ilimin mu abinda ya nuna mana kenan.

“Dukan su bayin Allah ne na gargaru ba'a taɓa kafiri ba. Wasu suna cewa, ai Ibrahim Baban sa Azara ne, sai muce eh, Baban sa akace ba Mahaifin sa ba akwai banbanci tsakanin 'ABU' da 'WALID' a larabci, idan ance Walid mahaifi kenan, idan ance Abu, Abba, yana zuwa ɗan uwan Uba ko kuma ma mahaifin Uwa duk ana ce masa Abbu amma ba'a ce masa Waalid.

“Ruwayar da wasu suke ta wasa da shi suke cewa wai 'Abi wa Abaka Finnar' (Wa'iyazibillah) suka danganta wannan zuwa Manzon Rahama kuma har sukayi magana mummuna dangane da wannan bawan Allah Abdullah (As) koda yake wasu sukan musu raddi suce ai ABBAH akace ba'a ce WALID ba. 

“Kuma idan ma ya inganta abinda yake nufi Manzon Rahama yana jin tausayin wannan mutumin ne, yayi masa Mujamala yace 'Abu wa Abaka Finnar', ai Abu Lahabi yake nufi. Domin Abu Lahab uba ne ga Annabi amma ba mahaifin sa ba. Amma Abdullahi bawa ne me tsarki, Amina baiwa ce me tsarki. Dukkan su bayi ne masu tsarki tun daga Adamu da Hauwa'u har ya zuwa Abdullahi da Amina haka kuma har ya zuwa Abdulmuɗalif da Fatimah bint Asad”

Post a Comment

0 Comments