Hukumar NAFDAC,Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Farashin Magunguna Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A ‘Yan Kwanakin Nan.

 Hukumar NAFDAC,Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Farashin Magunguna Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A ‘Yan Kwanakin Nan



Darakta Janar a Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan tsokaci a wani taron lacca na yanar gizo da jaridar The Cable ta shirya domin murnar cika shekaru 10 da kafuwa.

Sai dai ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za a fara duba matakan tsare tsare daban daban da gwamnati ta sanya a kan farashin kayayyakin kiwon lafiya.

Domin cimma wannan buri, shugabar ta NAFDAC ta jaddada bukatar sake farfado da masana’antar harhada magunguna ta cikin gida a matsayin hanyar da zata magance tsadar magunguna a kasar nan, inda ta kara da cewa magungunan da ake samar wa a cikin gida za su fi sauki da araha idan aka kwatanta da magungunan da ake shigowa da su daga kasashen ketare.

Farfesa Adeyeye ta nanata cewa hukumar NAFDAC karkashin jagorancinta ta fara shirin “5 plus 5” domin karfafa gwiwar masana’antar harhada magunguna ta cikin gida wajen bunkasa hanyoyin samar da magunguna

 

Post a Comment

0 Comments