Jami'an Najeriya sun bukaci mu basu cin hanci inji shugaban kamfanin Binance

 Jami'an Najeriya sun bukaci mu basu cin hanci inji shugaban kamfanin Binance 



Daga Mahadi Umar kaita

Jami’an Najeriya Sun Bukaci mu  Basu Cin Hanci 

Babban Jami’in Gudanarwa Shugaban kamfanin Binance, sanannen dandalin ciniki na cryptocurrency, Richard Teng, ya yi iƙirarin cewa wasu mutanen da ba a san su ba sun nemi cin hancin cryptocurrency daga shugabannin zartarwa na kamfanin.

Sun nemi a Basu cin hancin ne kafin su tsare ma'aikatan nasu guda biyu a ranar 28 ga Fabrairu, 2024, Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla.

 Teng ya baiyana Hakan a cikin shafinsa na yanar gizo a yau  Talata, akan Manhajar yanar gizon ta  Binance.



Post a Comment

0 Comments