Jami'an tsaro suna cin zarafin Mata da sunan dokar hana saka hijabi a Dungun mu'azu.
Daga Mahadi Umar kaita
Mutanen garin Dungun Mu'azu dake karamar hukumar sabuwa jihar katsina sun koka akan yacce jami'an tsaro ke tsawwala masu Akan dokar hana saka hijabi a yankin.
Tun mako biyu da suka gabata aka Saka dokar hana saka hijabi daga karfe biyar na yamman ko wace rana a cikin garin na Dungun Mu'azu
Muryar Labarai ta samu zantawa da wasu mutane da suka rayuwa a cikin garin Inda suka bayyanawa Muryar Labarai cewa ana rufe wacce dukkan macen da aka gani da hijabi da Duka ne batare da sauraron wani uzuri ba.
Wannan doka ta rashin yawo da hijabi daga bakin karfe 5na yamma har zuwa 7na safe ta samo asali ne akan yanayin tsaro da ake fama dashi a yankin.
Saidai kuma jami'an tsaro suna anfani da wannan damar ne wajen cin zarafin mata ta hanyar rufe duk wacce suka gani da hijabi da Duka ba tare da sun kar6i uzurin nata ba.
Wata baiwar Allah data nemi a sakaya sunanta tace "Muna cikin zullumi bamuda yancin fita daga bakin karfe biyar na yamma Wanda Wani lokacin fitar takan kama dole ne Kuma mu bazasu iya fita babu hijabi ba domin wannan karya dokar Allah, Wanda ita Daman wannan Gwamnatin abunda tasa gaba kenan yaki da dokokin Allah, hakika wannan abun zalunci ne kawai domin mutanen nan yaki suke da Musulunci saboda ansan inda Yan ta'addan nan suke.
Ta Kara da cewa dayake Muna a bayan gari ne kusa da bakin hanya duk sadda Yan Ta'addan nan zasu tafi wajen ta'addancinsu sukanbi ta hanya ne ta gaban mutane batare da an dauki wani mataki ba Amman sai aka fake da Hana Saka hijabi don zalunci.
Idan ance mutanen nan suna Saka hijabi ne tohm minene hadin mace da za'a hanata Saka hijabi Wanda shine yancinta Wanda Allah (T) ya bata ta saka domin taje duk inda takeso.
Ta Kara da cewa wannan zalunci ne Amman anyi shiru saboda ana tsoron mahukunta, kullum suna Kara gallaza mana ne da suna. Yaki da ta'addanci bayan mutanen nan bakinsu Daya.
0 Comments