Najeriya ta ɗauki ƙwararan matakan daƙile hadahadar Naira a manhajojin Crypto


Hukumar kula da harkokin kasuwanci ta ta ƙasa Najeriya, Security and Exchange Commission (SEC), tace ta fara cire naira daga dandalin kasuwanci na peer-to-peer (P2P) a manhajojin Crypto. 

SEC, a makon da ya gabata tare da haɗin gwiwar ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (ONSA), ya umarci masu sarrafa kuɗin dijital da su cire Naira daga dandamalin su a matsayin wani ɓangare na matakan kare darajar kuɗin ƙasar.

A wani rahoton da Vanguard ta wallafa, tace Hukumar ta bayyana cewa binciken ta ya nuna cewa an cire Naira cikin hada-hadar kudi a dandalin KuCoin kuma tuni aka fara yin gyare-gyaren da ya kamata a kan fasahar.

Hukumar na sa ran cire naira daga dandali zai kara karfafa darajar kuɗin ƙasar. 

Mukaddashin Darakta Janar na SEC, Dokta Emomotimi Agama, wanda ke mayar da martani game da cirewar KuCoin, ya nuna farin ciki cewa musayar crypto suna bin umarnin ONSA da SEC, ya kwatanta abin a matsayin wani abin alfahari a ƙasar. 

Post a Comment

0 Comments