Sama da ma'aikata 1,000 sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Birtaniya

 Sama da ma'aikata 1,000 suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa, inda suka toshe Ma’aikatar Cinikayya ta Birtaniya da ke Landan



Sama da ma'aikata 1,000 sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Birtaniya

Sama da ma’aikata dubu ɗaya a faɗin Birtaniya suka gudanar da zanga-zanga a Ranar Ma’aikata ta Duniya inda suke kira kan a daina sayar wa Isra’ila makamai.

Ma’aikatan sun toshe Ma’aikatar Cinikayya ta Birtaniya da ke Landan da wasu kamfanonin makamai da ke Scotland da Wales da Lancashire.

A Landan, masu zanga-zangar sun buƙaci gwamnatin ƙasar ta ƙwace lasisin fitar da makamai ga Isra’ila daga kamfanonin ƙasar.

A ɗayan ɓangaren kuwa, mambobin ƙungiyar goyon bayan Falasɗinawa ta Palestine Action group ta yi zanga-zanga a gaban ofisoshin bankunan Barclays da BNY Mellon da ke Manchester inda ƙungiyar ke zarginsu da alaƙa da Isra’ila


Post a Comment

0 Comments