Shugaban Nijeriya Tinubu zai ƙaddamar da tasoshin sarrafa iskar gas uku a ƙasar

Shugaban Nijeriya Tinubu zai ƙaddamar da tasoshin sarrafa iskar gas uku a ƙasar

An kulla yarjejeniyar ne don rarraba makamashin iskar gas mafi tsafta da inganci ga masana'antu a jihar.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu na shirin kaddamar da wasu masana’antun sarrafa iskar gas guda uku wadanda za su bunkasa samar da iskar gas ga kasuwannin cikin gida na ƙasar zuwa kubik miliyan 500 a kowace rana, tare da kuma inganta zuba jari a kasar.

Ayyukan, waɗanda Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) da abokan hadin gwiwa ke gudanarwa, za a yi su ne don tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin tarayya na inganta darajar ɗaga kadarorin iskar gas na ƙasa tare da rage hayaƙin ƙona iskar gas.

An bayyana hakan ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale.

Ya bayyana cewa, an hanzarta kai ayyukan tun daga farkon gwamnatin Shugaba Tinubu wajen ɗorewar manufar zurfafa samar da iskar gas a cikin gida a matsayin hanyar bunkasa tattalin arziki.

Shell ya sa hannu kan yarjejeniyar bututun iskar gas na dala miliyan $100m da jihar Oyo ta Nijeriya

A wani labarin na daban kuma, Kamfanin Shell a Nijeriya ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da jihar Oyo da ke kudancin kasar domin gina tsarin isar da bututun mai da zai yi hidima ga masana’antu a jihar kan kudi dala miliyan 100, kamar yadda gwamnatin Oyo ta bayyana a ranar Juma’a.

Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a Landan tare da Shell Nigeria Gas (SNG) na da matukar muhimmanci ga kokarin da jihar ke yi na bunkasa masana'antu da ci gaban tattalin arziki tare da inganta samar da wutar lantarki ga wuraren zama da masana'antu.

Post a Comment

0 Comments