Ƙungiyar ƙwadago na neman gwamnatin Najeriya ta mayar da mafi ƙarancin albashi N615,000 daga N30,000 da yake a yanzu, kuma ta ba ta wa'adin ranar 29 ga watan Mayu
'Yan Najeriya da dama sun zaƙu su ga adadin abin da gwamnati ta yanke a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi, amma idan aka duba tarihi za a ga cewa irin wannan jan-ƙafar ba sabon abu ba ne.
Sai dai 'yan ƙasar sun wayi garin ranar Laraba - ranar ma'aikata - da sanarwar cewa gwamnatin tarayya ta ƙara wa ma'aikanta kashi 25 zuwa 35 cikin 100 na albashinsu. Amma haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta ce wannan ba shi cikin tattaunawar da suke yi da gwamnatin a yanzu.
Yanzu haka dai ƙungiyar na neman gwamnatin ta mayar da mafi ƙarancin albashin N615,000 daga N30,000 da yake a yanzu, kuma ta ba ta wa'adin ranar 29 ga watan Mayu.
Tun a watan Afrilun 2019 gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da fara biyan N30,000 ɗin - wanda bai wuce dalar Amurka $21.50 ba.
0 Comments