Yan bindiga shiga garin Bilbis da yammacin yau din nan Alhamis sun kashe mutane sama da 20

 Tashin Hankali: Yan bindiga shiga garin Bilbis da yammacin yau din nan Alhamis sun kashe mutane sama da 20


A rahotannin da Katsina Daily News ke samu a Yammacin yau Alhamis, yan bindiga sun shiga yankin garuruwan Bilbis karamar hukumar Tsafe da ta hada iyaka da Bilbis ta karamar hukumar Faskari, inda sukai ta harbin kan mai uwa da wabi, ana tattara gawarwaki 20 kamar yadda wani mazaunin yankin ya tabbatar wa Katsina Daily News. 

Kamar yadda majiyar tamu ta rawaito, wasu gungun yan bindiga su uku bisa mashin daya suka fara shigowa garin Bilbis ta Faskari ana sallar la'asar suka ƙetare zuwa Bilbis ta Zamfara da rafi ne kawai ya raba garuruwan, bayan sun je suka dira wani masallaci har suka cacike limamin ana tsaka da sallah

Bayan sun gama ba tare da sun yi wa jama'a komai ba, dai suka koma, komawar su ke da wuya sai ga wasu babura akalla guda bakwai da goyon uku uku, can kuma dai ga wasu kudan goma suma dauke da bindigu, suka datse hanyar Bilbis suka ci gaba da harbin duk wanda ya bullo ta hanyar. 

Aƙalla sun kashe sama da mutum 20, tare da raunata mutane da dama, sannan suna cewa ba wajen yan Bilbis ta Faskari suka zo ba, sun zo ne wajen yan Bilbis ta Zamfara" Kamar yadda Katsina Daily News ta samu

Post a Comment

0 Comments